-
MDD: Saudiyya Tana Hana Ba Wa Jiragen Agaji Zuwa Yemen Mai
Aug 02, 2017 06:35Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa gwamnatin Saudiyya tana ci gaba da hana ba wa jiragen saman agajinta man fetur din da suke bukata wajen ci gaba da kai kayayyakin agaji ga al’ummar kasar Yemen a babban birnin kasar Sana’.
-
Bukatar Jamus Ga Tarayyar Turai Na Ta Dauki Mataki A Kan Amurka
Aug 02, 2017 03:22Ministan harkokin tattalin arziki na kasar Jamus ta bayyana cewa takunkuman tattalin arzikin da Amurka ta dorawa kasar Rasha basa bisa ka'ida sun kuma sabawa dokokin kasa da kasa, ta kuma bukaci tarayyar Turai ta dauki mataki na maida martani kan Amurkan.
-
China Ta Kafa Sansanin Sojan Ruwa A Kasar Djibouti
Aug 02, 2017 02:07Kasar china ta kafa sansanin sojin ruwa na farko a kasashe wajen a kasar Djibouti.
-
Venezuela : An cafke Jagororin 'Yan Adawa Saboda Yunkurin Tserewa
Aug 01, 2017 13:03Kotun koli a Venezuela ta ce an cafke jagoririn 'yan kasar biyu saboda yunkurin ficewa daga kasar, alhali daurin talala na a kan su.
-
Kasashen Musulmi Sunyi Tir Da Halin Tsokana Na H.K. Isra'ila
Aug 01, 2017 12:43Wakilan kasashen musulmi 57 na kungiyar OIC da suka taru yau a birnin Satambul na Turkiyya sunyi tir da abunda suka kira tsokana na yahudawan mamaya na Isra'ila a masallacin Al'Aqsa dake birnin Qudus.
-
Jamus Ta Yi Kakkausar Suka Kan Sabbin Takunkuman Amurka A Kan Rasha
Aug 01, 2017 02:58Gwamnatin kasar Jamus ta yi kakkausar suka dangane da sabbin takunkuman da Amurka ta dora wa kasar Rasha, tare da bayyana hakan da cewa ya sabawa ka'ida.
-
Amurka Da Japan Sun Damu Akan Barazana Koriya Ta Arewa
Aug 01, 2017 00:28Kasashen Amurka da Japan sun damu matuka akan yadda Koriya ta Arewa ta zamo babbar barazana bayan gwajin makamin linzami mai cin dogon zango data yi a ranar Juma'a data gabata.
-
Harin Bindiga Yayi Sanadiyar Mutanwar Mutane Biyu A Jamus
Jul 30, 2017 07:24Harin bindiga da aka kai wajen gidan wani rawa daren jiya assabar a kasar Jamus yayi sanadiyar mutuwar mutane biyu tare da jikkata wasu da dama na daban.
-
Bukatar Mazauna Yankin Awamiya na Kasar Saudiya Daga MDD
Jul 30, 2017 07:23A yayin da Jami'an tsaron Saudiya ke ci gaba da kai farmaki kan mazauna yankin Awamiya da suka kasance mabiyar mazhabar Shi'a, mazauna yankin sun bukaci MDD da ta shga tsakani domin kawo karshen wannan lamari.
-
Otawa Ta Damu Akan Zargin Saudiyya Na Cin Zarafin Bil Adama Da Kayan Yakin Canada
Jul 30, 2017 01:53Mahukuntan Otawa sun nuna matukar damuwa dangane da zargin cewa ko Saudiyya na amfani da motoci masu sulke kirar kasar ta Canada don cin zarafin bil adama a gabashin kasar.