MDD: Saudiyya Tana Hana Ba Wa Jiragen Agaji Zuwa Yemen Mai
Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa gwamnatin Saudiyya tana ci gaba da hana ba wa jiragen saman agajinta man fetur din da suke bukata wajen ci gaba da kai kayayyakin agaji ga al’ummar kasar Yemen a babban birnin kasar Sana’.
Babban daraktan shirin agaji na MDD a kasar Yemen Auke Lootsma ne ya sanar da hakan inda ya ce a halin yanzu jiragen hukumar guda biyu da suke kai kayayyakin agaji zuwa birnin Sana’a din daga kasashen Jordan da Djibouti suna nan a birnin San’a saboda rashin mai.
Babban daraktan ya ci gaba da cewa: Muna fuskantar matsalolin gaske wajen samun izinin safarar man fetur daga wajen sojojin hadin gwiwa (karkashin jagorancin Saudiyya) don zubawa a wadannan jirage don su ci gaba da ayyukansu na agaji.
Wannan dai ba shi ne karon farko da MDD take nuna damuwa dangane da irin kafar ungulun da Saudiyya da kawayenta suke yi ga ayyukan agaji da take gudanarwa a kasar Yemen din da al’ummar kasar suke bukatar agaji na gaggawa sakamakon ci gaba da hare-haren da Saudiyya da kawayenta suke kai wa Yemen din.