Harin Bindiga Yayi Sanadiyar Mutanwar Mutane Biyu A Jamus
Harin bindiga da aka kai wajen gidan wani rawa daren jiya assabar a kasar Jamus yayi sanadiyar mutuwar mutane biyu tare da jikkata wasu da dama na daban.
Kamfanin dillancin labaran Jamus ya nakalto jami'an 'yan sandar kasar na cewa a daren jiya Assabar wani dan bindiga ya buda wuta a wani gidan rawa na garin Constance dake jihar Baden Wurttemberg, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyu tare da jikkata wasu da dama na daban.
Har yanzu ba a bayyana dalilin kai wannan hari ba.
Bisa rahoton jami'an 'yan sanda, wanda ake zarkin kai harin, matashi ne mai shekaru 34 a duniya, kuma bayan fitowar sa daga cikin gidan rawan jami'an 'yan sanda sun bindige shi, inda ya samu mumunan rauni sannan ya cika bayan an isa asibiti.