Amurka Da Japan Sun Damu Akan Barazana Koriya Ta Arewa
https://parstoday.ir/ha/news/world-i22768-amurka_da_japan_sun_damu_akan_barazana_koriya_ta_arewa
Kasashen Amurka da Japan sun damu matuka akan yadda Koriya ta Arewa ta zamo babbar barazana bayan gwajin makamin linzami mai cin dogon zango data yi a ranar Juma'a data gabata.
(last modified 2018-08-22T07:00:28+00:00 )
Aug 01, 2017 00:28 UTC
  • Amurka Da Japan Sun Damu Akan Barazana Koriya Ta Arewa

Kasashen Amurka da Japan sun damu matuka akan yadda Koriya ta Arewa ta zamo babbar barazana bayan gwajin makamin linzami mai cin dogon zango data yi a ranar Juma'a data gabata.

A yayin wata tattaunawa ta wayar tarho tsakanin shugaba Donald Trump na Amurka da firayi ministan Japon Shinzo Abe, kasashen sun jaddada yadda koriya ta Arewar ke zama babbar barazana ga Amurka, Japon da Koriya ta Kudu dama wasu kasashe na kusa da ita da na nesa.

Bangarorin biyu sun dau matakin kara karfafa takunkuminsu  akan gwamnatin ta Pyangyang tare da shan alwashin shawo kan wasu kasashe akan daukar irin wannan matakin.