Bukatar Mazauna Yankin Awamiya na Kasar Saudiya Daga MDD
https://parstoday.ir/ha/news/world-i22732-bukatar_mazauna_yankin_awamiya_na_kasar_saudiya_daga_mdd
A yayin da Jami'an tsaron Saudiya ke ci gaba da kai farmaki kan mazauna yankin Awamiya da suka kasance mabiyar mazhabar Shi'a, mazauna yankin sun bukaci MDD da ta shga tsakani domin kawo karshen wannan lamari.
(last modified 2018-08-22T07:00:28+00:00 )
Jul 30, 2017 07:23 UTC
  • Bukatar Mazauna Yankin Awamiya na Kasar Saudiya Daga MDD

A yayin da Jami'an tsaron Saudiya ke ci gaba da kai farmaki kan mazauna yankin Awamiya da suka kasance mabiyar mazhabar Shi'a, mazauna yankin sun bukaci MDD da ta shga tsakani domin kawo karshen wannan lamari.

Kamfanin dillancin labaran Meher na kasar Iran ya habarta cewa a yayin da farmakin  jami'an tsaron Saudiya ke kara tsanani kan al'ummar yankin Awamiya na garin Katif dake  jihar Asharkiya, mazauna yankin sun bukaci kungiyoyin kasa da kasa na kare hakin bil-adama da su tura tawaga ta musaman zuwa yankin domin gudanar da bincike kan irin take hakin da Gwamnatin Saudiya ke yi musu

A harin baya-bayan nan da jami'an tsaron Saudiya suka kaiwa mazauna yankin Awamiya 'yan shi'a da ke garin Katif, mutane da dama ne suka jikkata daga cikin su har da mata da kananen yara.

Tun daga ranar 10 ga watan Mayun da ya gabata ce, jami'an tsaron Saudiyar suka tsananta kai hare-haren su ga mazauna yankin Awamiya na garin Katif da nufin rusa wuraren gwagwarmaya na yankin.