-
An Tsaurara Matakan Tsaro A New York Gabannin Taron Babbar Zauren MDD
Sep 19, 2016 06:52Sakamakon harin ta'addancin da aka birnin New York na Amurka, ma'aikatar tsaron cikin gidan Amurka ta sanar da daukan tsauraran matakan tsaro a duk fadin birnin a daidai lokacin da ake shirin fara gudanar da taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya inda ake sa ran shugabannin kasashe da dama za su halarta.
-
Amurka : An Cafke Mutane Biyar Bayan Tashin Bam A New York
Sep 19, 2016 01:20Rahotanni daga Amurka na cewa an cafke mutane biyar bayan tashin bam da aka samu a birnin Chelsea a jiya.
-
Jam’iyyar Putin Tayi Rinjaye A Zaben 'Yan Majalisa
Sep 19, 2016 01:04Rahotanni daga Rasha na cewa Jam’iyyar shugaban kasar Vladimir Putin na sahun gaba da gagarimin rinjaye a zaben 'yan majalisar dokokin kasar da aka kada kuri'arsa jiya lahadi.
-
An Rufe Wasannin Paralympics Cikin Jimami
Sep 19, 2016 00:46Rahotanni daga birnin Rio de Janairo na Brazil na cewa an rufe wasannin Paralympics na nakassasu tare da halartar dubban masu kallo da suka halarci bikin da aka shirya na kashe wutar wasannin a filin wasa na Maracana.
-
Taron Koli Na MDD Kan Kwararar Bakin Haure
Sep 19, 2016 00:46A wani lokaci a yau Litinin ne ake sa ran kasashe 193 mambobin MDD, zasu nemi cimma matsaya guda akan yadda zasu tunkari matsalar kwararar bakin haure .
-
Rasha: Harin Amurka Yayi Sanadiyyar Mutuwar Sojojin Siriya 62
Sep 18, 2016 06:39Kasar Rasha ta tabbatar da cewa wasu sojojin kasar Siriya su 62 sun rasa rayukansu sakamakon harin da jiragen yakin kawancen kasashen Yammaci da nufin fada da ta'addanci suka kai musu a kusa da filin jirgin saman soji na Dayr al Zawr da ke kewaye da 'yan kungiyar Daesh.
-
Wasu Mutane Masu Yawa Sun Sami Rauni A Fashewar Wani Abu A Birnin New York
Sep 18, 2016 06:38Rahotanni daga kasar Amurka sun bayyana cewar alal akalla mutane 29 sun sami raunuka sakamakon fashewar wani abu a gundumar Chelsea da ke Manhattan na birnin New York na Amurkan.
-
Zaman Gaggawa Da Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya Ya Gudanar Kan Kasar Siriya
Sep 18, 2016 00:58Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar da zaman gaggawa a cikin daren jiya wayewar garin yau Lahadi kan matsalar kasar Siriya amma zaman ya kawo karshe ba tare da cimma wata kwakkwarar matsaya ba.
-
Siriya : Halin Da Ake Ciki Na Kara Tabarbarewa, Inji Rasha
Sep 17, 2016 10:09Rundunar sojin kasar Rasha ta bayyana cewa halin da ake ciki a Siriya na kara tabarbarewa, bayan da aka kai hare-hare sama da hamsin akan cibiyoyin dakarun kasar Siriya da kuma fararen hula a kasa da sa'o'i 24.
-
Iran: Karyar Alkawarin Yammaci, Zai Yi Barazana Ga Yarjejeniyar Nukiliya
Sep 17, 2016 06:20Shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya na Iran Dakta Ali Akbar Salehi ya bayyana cewar har ya zuwa yanzu dai kasashen yammaci suna ci gaba da karen tsaye ga yarjejeniyar nukiliyan da Iran ta cimma da su wanda hakan yana iya barazana ga ci gaba da wanzuwar yarjejeniyar.