Siriya : Halin Da Ake Ciki Na Kara Tabarbarewa, Inji Rasha
Rundunar sojin kasar Rasha ta bayyana cewa halin da ake ciki a Siriya na kara tabarbarewa, bayan da aka kai hare-hare sama da hamsin akan cibiyoyin dakarun kasar Siriya da kuma fararen hula a kasa da sa'o'i 24.
Wata sanarwa da rundinar sojin kasar Rasha ta fitar yau Asabar ta dora al'hakin dukkan abun da ke faruwa akan kasar Amurka wace ta kasa tabaka komai domin ganin yarjejeniyar tsagaita wuta da suka shata tsakaninsu ta daure.
Da yake bayyana halin da ake ciki, Jagoran cibiyar dake kula da ayyukan soji na Rasha a kasar ta Siriya, Vladimir Savtchenko, ya ce lamarin ya fi shafar yankunan Halep da kuma Hama inda 'yan tawayen kasar ke amfani da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma suna harhada kayan yaki tare da yin sabon shiri don farmawa wasu yankuna da nufin kwace su.
Hakazalika a cewarsa a cikin sa'o'i 24 kadai da suka wuce an kashe fararen hula 12 ciki har da yara kanana guda biyu tare da raunana wasu sama da 40.
kasar Rasha dai ta sake zargin Amurka da rashin cika al'kawarin data dauka dangane da yarjejeniyar tsagaita wuta da suka cimma a ranar tara ga watan nan a Geneva, tare da cewa Amurka ita sila idan har yarjejeniyar data fara aiki a ranar Litinin bata haifar da ''da mai ido ba''