Taron Koli Na MDD Kan Kwararar Bakin Haure
A wani lokaci a yau Litinin ne ake sa ran kasashe 193 mambobin MDD, zasu nemi cimma matsaya guda akan yadda zasu tunkari matsalar kwararar bakin haure .
Shugabannin kasahen zasu kuma tattaunawa akan yakin da aka kwashe shekara biyar ana yi a kasar Siriya wanda kawo yanzu ya yi sanadin mutuwar mutane sama da dubu dari uku tare da cilastawa wasu mutanen sama da miliyan hudu yin gudun hijira a kasashen makofta ko kuma turai.
Za'a kuma tattauna halin da ake ciki kan yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a wannan kasa ta Siyira, wace kawo yanzu take cikin tangal-tangal.
Ana sa ran kasahen duniya zasu fitar da wata sanarwa yau Litinin a daura da taron koli na MDD da za'a somawa gobe Talata.
Bayanai sun nuna cewa za'a fifuita batutuwan da suka hada da mutunta incin bakin haur, haddin gwiwar kasa da kasa akan yaki da safara da kyamma da kuma samar da ilimi ga yara bakin haure.
Tun da farko dai MDD ta bakin babban sakataren ta Ban ki Moon ta nemi ga ko wace kasa ta dinga karbar kashi 10% na adadin bakin haure, saidai wannan yunkurin ya cutura inda kasahen suka mika shi wannan batun har zuwa shekara 2018, lamarin da ke shan suka daga kungiyoyin kasa da kasa.