Rasha: Harin Amurka Yayi Sanadiyyar Mutuwar Sojojin Siriya 62
https://parstoday.ir/ha/news/world-i11200-rasha_harin_amurka_yayi_sanadiyyar_mutuwar_sojojin_siriya_62
Kasar Rasha ta tabbatar da cewa wasu sojojin kasar Siriya su 62 sun rasa rayukansu sakamakon harin da jiragen yakin kawancen kasashen Yammaci da nufin fada da ta'addanci suka kai musu a kusa da filin jirgin saman soji na Dayr al Zawr da ke kewaye da 'yan kungiyar Daesh.
(last modified 2018-08-22T06:58:56+00:00 )
Sep 18, 2016 06:39 UTC
  • Rasha: Harin Amurka Yayi Sanadiyyar Mutuwar Sojojin Siriya 62

Kasar Rasha ta tabbatar da cewa wasu sojojin kasar Siriya su 62 sun rasa rayukansu sakamakon harin da jiragen yakin kawancen kasashen Yammaci da nufin fada da ta'addanci suka kai musu a kusa da filin jirgin saman soji na Dayr al Zawr da ke kewaye da 'yan kungiyar Daesh.

Kasar Rashan ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar a yau din nan inda ta ce jiragen saman yakin Kawancen kasa da kasa na fada da ta'addanci sun kai wasu hare-hare guda hudu kan sojojin Siriya da suke filin jirgin saman soji na Dayr al-Zawr da 'yan ta'addan Da'esh suka yi wa kawanya lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar sojojin Siriyan 62 kana wasu da dama kuma suka sami raunuka.

Ma'aikatar tsaron Amurka (PENTAGON) cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce jiragen yakin kasar ne suka  kai hari amma bisa kuskure ne bisa tunanin cewa sansanin 'yan ta'addan Da'esh ne.

To sai dai kuma kasar Rasha da ma gwamnatin Siriyan ta sa shakku cikin wannan ikirarin kuskure na Amurka saboda a cewar sanarwar Rashan jin kadan bayan kai harin 'yan ta'addan Da'esh din suka kaddamar da wasu hare-hare kan sojojin Siriyan abin da ke nuni da cewa akwai wani shiri tsakaninsu da Amurkan.

Gwamnatin Siriyan dai ta yi Allah wadai da wannan harin tana mai cewa hakan wani kokari ne na Amurkan wajen taimakon 'yan ta'addan na Da'esh.