An Rufe Wasannin Paralympics Cikin Jimami
Rahotanni daga birnin Rio de Janairo na Brazil na cewa an rufe wasannin Paralympics na nakassasu tare da halartar dubban masu kallo da suka halarci bikin da aka shirya na kashe wutar wasannin a filin wasa na Maracana.
A wasannin da aka kammalla Jiya Lahadi birnin Rio na kasar Brazil ya mikawa birnin Tokiyo na Japon tutar shirya wasannin masu zuwa a 2020.
Bayan shafe kwanaki 11 na fafatawa a tsakanin ‘yan wasa daga kasashen duniya daban daban, kasar China ce tafi samun nasarori masu yawa inda ta samu lambobin yabo na zinariya 106. .
Saidai a wannan karo an rufe wasannin cikin jimami bayan rasuwar wani dan wasan tseren keke na nakassasu dan kasar Iran wanda ya rasa ransa bayan raunin da ya samu sakamakon munmunar faduwa da yayi a yayin da ake tsakiya gasar tseren keke a ranar asabar.
Sanarwar da kwamitin wasannin Olympics ya fitar, ta nuna alhininta kan mutuwar dan wasan Bahman Golbarnezhad, inda ya meka sakon ta’azziya ga kasar Iran da kuma iyalansa.
ko baya ga hakan dai a Jiya Lahadi an rage tsawan tutotin Iran da kuma na Paralympique, kana kuma anyi tsit na minti guda domin martaba mamacin dan shekaru 48 a duniya.