Iran: Karyar Alkawarin Yammaci, Zai Yi Barazana Ga Yarjejeniyar Nukiliya
(last modified Sat, 17 Sep 2016 10:50:10 GMT )
Sep 17, 2016 10:50 UTC
  • Iran: Karyar Alkawarin Yammaci, Zai Yi Barazana Ga Yarjejeniyar Nukiliya

Shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya na Iran Dakta Ali Akbar Salehi ya bayyana cewar har ya zuwa yanzu dai kasashen yammaci suna ci gaba da karen tsaye ga yarjejeniyar nukiliyan da Iran ta cimma da su wanda hakan yana iya barazana ga ci gaba da wanzuwar yarjejeniyar.

Dakta Salehi ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da jaridar The Guardian ta kasar Birtaniyya inda ya ce akwai yiyuwar yarjejeniyar ta shiga cikin wani mawuyacin hali sakamakon irin maganganun da 'yan takaran shugabancin Amurka suke yi kan yarjejeniyar yana mai cewar gaza aiwatar da yarjejeniyar a bangaren kasashen yammacin na iya yin barazana ga ci gaba da wanzuwar yarjejeniyar.

Shugaban hukumar nukiliyan ta Iran ya kara da cewa: Jagoran juyin juya halin Musulunci ya taba cewa Iran ba za ta karya yarjejeniyar ba, to amma kuma za ta yi watsi da ita matukar daya bangaren ya ci gaba da karya abin da aka cimma a yarjejeniyar.

Cikin 'yan kwanakin nan dai 'yan takaran shugabancin Amurka a zaben da za a gudanar a kasar a watan Nuwamba suna ta magana kan yarjejeniyar musamman dan takaran jam'iyyar Republican Donald Trump wanda ya ce zai yi watsi da yarjejeniyar in ya hau mulkin Amurkan.