-
An Yi Maraba Da Murabus Da Shugaban Tawagar 'Yan Tawayen Siriya Ya Yi Daga Mukaminsa
May 30, 2016 12:36Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha ya bayyana cewa murabus da shugaban tawagar 'yan tawayen kasar Siriya da suke samun cikakken goyon bayan masarautar Saudiyya Muhammad Alush ya yi daga matsayinsa a zaman tattaunawan sulhu a birnin Geneva zai taimaka wajen cimma daidaiton baki a zaman tattaunawan.
-
Kungiyar Kwallon Kafa Ta Real Madrid Ta Zama Zakaran Turai
May 29, 2016 11:46Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta kasar Spain ta lashe gasar zakara zakarun Turai bayan ta lallasa abokiyar karawarta wato kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid ita ma dai ta kasar Spain din.
-
Neman Uzuri shine sharadin falfado da alakar kasashen Turkiya da Rasha
May 29, 2016 06:37ShUgaban Kasar Rasha ya ce idan kasar Turkiya tana so da falfado alakatar ta da kasar wajibi ne ta nemi afuwa daga kasar ta Rasha
-
MDD Ta Yi Maraba Da Tattaunawar Siyasa A Burundi
May 29, 2016 01:08MDD tayi maraba da tattaunawar siyasa da aka yi a kwanan baya a birnin Arusha dake arewacin kasar Tanzania kan rikicin siyasa kasar Burundi daya ki yaki cinyewa.
-
WHO ta goyi bayan a gudanar da Wasanin Olympic na RIO
May 28, 2016 06:41Kungiyar Lafiya ta Duniya ta ce Cutar Zika ba za ta hana a soke ko kuma sauya wurin wasannin Olympic din ba a kasar Brazil
-
Putin Ya Ce Ba Za Su Bar Kasar Siriya Ta Zama Kamar Kasashen Libiya Da Somaliya Ba
May 28, 2016 01:10Shugaban kasar Rasha ya bayyana cewa; Ba zasu taba zuba ido su kyale masu mummunar aniya su cimma burinsu na ganin kasar Siriya ta zame kamar yadda kasashen Libiya da Somaliya suka kasance a halin yanzu ba.
-
Ban Ki-Moon Ya Jaddada Muhimmancin Zama Tsakanin Gwamnati Burundi Da 'Yan Adawar Kasar
May 28, 2016 01:08Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya jaddada muhimmancin gudanar da zaman tattaunawa na kai tsaye tsakanin gwamnatin Burundi da 'yan adawar kasar.
-
Obama ya Ziyarci Hiroshima
May 27, 2016 13:43Shugaban Amurka Barack Obama ya ziyarci birnin Hiroshima na kasar Japan, wanda Amurka ta kai wa hari da makamin nukiliya a lokacin yakin duniya na biyu.
-
An Samu Tashin Farashin Mai A Kasuwar Mai Ta Duniya
May 27, 2016 00:41Rahotanni sun bayyana cewar a karon farko a shekarar 2016 an sami tashin farashin man fetur zuwa dalla 50 kan kowace gangar danyen man hakan kuwa ya biyo bayan yawaitar bukatarsa ne a kasashen duniya.
-
Gwamnatin Aljeriya Ta Bada Umurnin Rufe Gidajen Talabijin Da Dama A Kasar
May 26, 2016 13:36Fira ministan Aljeriya ya bada umurnin rufe gidajen talabijin musamman masu zaman kansu da dama a duk fadin kasar a karkashin sabon shirin da gwamnatinsa ta bullo da shi a fagen yada labarai.