Neman Uzuri shine sharadin falfado da alakar kasashen Turkiya da Rasha
ShUgaban Kasar Rasha ya ce idan kasar Turkiya tana so da falfado alakatar ta da kasar wajibi ne ta nemi afuwa daga kasar ta Rasha
A cikin wani Jawabi da ya gabatar jiya Assabar Shugaban Kasar Rasha Viladimim Putin ya ce sharadin farfado da alaka tsakanin kasarsa da Turkiya shi ne magabatan na birnin Ankara su nemi afuwa kan lafin halbo jirgin yakin kasar a Siriya.
Matukar dai magabatan na Ankara ba su amince da wannan sharadi ba, alaka tsakanin kasashen biyu ba za kasance kamar yadda take a baya ba.
Shugaba Putin ya kara da cewa har yanzu ya kasa fahimtar dalilin da ya sanya kasar Turkiya ta halbo jirgin yakin kasar sa samfarin S-24 a sararin samaniyar kasar Siriya da kahan ya janyo tabarbarewar alaka tsakanin kasashen biyu.
Shugaban Rutun ya ce matsayin Rasha a fili yake, matukar magabatan Turkiyan na son medo da alakar dake tsakanin su kamar yadda take a baya, wajibi ne su nemi afuwa tare da biyan diyar jirgin yakin Rashan da suka halbo gami da yin alkawrin cewa ba za su sake aikata wannan kuskuran ba.