Obama ya Ziyarci Hiroshima
https://parstoday.ir/ha/news/world-i5863-obama_ya_ziyarci_hiroshima
Shugaban Amurka Barack Obama ya ziyarci birnin Hiroshima na kasar Japan, wanda Amurka ta kai wa hari da makamin nukiliya a lokacin yakin duniya na biyu.
(last modified 2018-08-22T06:58:21+00:00 )
May 27, 2016 13:43 UTC
  • Obama ya Ziyarci Hiroshima

Shugaban Amurka Barack Obama ya ziyarci birnin Hiroshima na kasar Japan, wanda Amurka ta kai wa hari da makamin nukiliya a lokacin yakin duniya na biyu.

Hakan dai ya sanya Obama zama wani shugaban Amurka na farko daya ziyarci wannan birnin bayan harin.

Obama wanda ke halartar taron kasashe 7 masu karfin tattalin arziki a kasar ta Japan, ya ziyarci garin na Hiroshima tare da dora furanni a wani dandali domin tunawa da sama da mutane dubu 140, da suka rasa rayukansu sakamakon wannan hari da kasar ta kai a ranar 6 ga watan agustan shekara ta 1945.

Kwana biyu kuma bayan hakan, Amurka ta sake kai hari a birnin Nagasaki lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum 74,000.

Har ila yau an tsara shugaban na Amurka zai gabatar da wani kwarya-kwaryan jawabi dangane da wannan lamari, duk da cewa Obama ba zai nemi afuwar Japan a game da wannan hari ba.