An Samu Tashin Farashin Mai A Kasuwar Mai Ta Duniya
(last modified Fri, 27 May 2016 05:11:57 GMT )
May 27, 2016 05:11 UTC
  • An Samu Tashin Farashin Mai A Kasuwar Mai Ta Duniya

Rahotanni sun bayyana cewar a karon farko a shekarar 2016 an sami tashin farashin man fetur zuwa dalla 50 kan kowace gangar danyen man hakan kuwa ya biyo bayan yawaitar bukatarsa ne a kasashen duniya.

Rahotannin sun ce hakan ya faru ne sakamakon wasu bayanai da Ma'aikatar makamashin Amurka ta fitar jiya Alhamis da ke nuna cewa yawan man da take da shi ya ragu saboda wutar dajin da ta tashi a kasar Canada wacce ita ce babbar mai samar wa Amurkan da man da take bukata, inda aka sayar da danyen mai samfurin Brent a kan dalla 50.07 a kasuwannin nahiyar Asiya.

Wutar dajin da ta tashi a yammacin kasar Kanadan dai ta tilasta mata rage yawan

man da take fitarwa da kimanin ganga miliyan daya a kullum, lamarin da ya sanya Amurkan a makon da ya wuce ta fuskanci matsalar raguwar man na ta da ganga miliyan 4 da dubu 200.

Har ila yau kuma wasu masanan harkar mai din sun bayyana cewar matsalar da Nijeriya take fuskanta wajen fitar da manta sakamakon hare-haren da ake kai bututun man kasar, bugu da kari kan rikicin siyasa da ke faruwa a kasar Venezuela wadanda dukkanin kasashen biyu suna daga cikin kasashen da suke fitar da man fetur zuwa kasuwannin duniya suna daga cikin lamurran da suka janyo karancin mai din a kasuwa lamarin da a dabi'ance zai sanya a samu tashin farashinsa.