WHO ta goyi bayan a gudanar da Wasanin Olympic na RIO
Kungiyar Lafiya ta Duniya ta ce Cutar Zika ba za ta hana a soke ko kuma sauya wurin wasannin Olympic din ba a kasar Brazil
Cikin wata Sanarwa da ta fiyar Yau Assabar Kungiyar ta yi watsi da kiran da kwararru kan kiwon lafiya suka yi na a janye wasannin Olympic daga birnin Rio saboda annobar cutar Zika.
A wata budaddiya wasika ga kungiyar ta WHO, kwararrun 150 daga kasashe da dama sun ce bai dace a gudanar da wasannin Rio din a watan Agusta ba saboda hadari ga lafiyar al'umma.
Amma a wata sanarwa, WHO din ta yi watsi da kiran da cewa a soke ko kuma sauya wurin wasannin ba zai hana yaduwar cutar ta Zika ba.
A cikin wata wasika da suka wallafa, kwararun da suka fito daga gwamman kasashe sun ce a fili take cewa akwai barazana kan lafiyar al'ummar kasashen duniya.
Sun yi kira ga WHO din da ta kafa wani kwamiti na kwararru da zai bai wa kwamitin shirya gasar wasan Olympic din shawarwari.
Kwayar cutar ta Zika dai na saka mata masu juna biyu haihuwar jarirai masu tawaya ko kuma gilo.