-
Ministan Harkokin Wajen Jamus Ya Jingine Batun Tafiyarsa Zuwa Saudiyya
Oct 18, 2018 02:22Ministan harkokin wajen kasar Jamus Heiko Maas ya dakatar da tafiyar da aka shirya cewa zai zuwa kasar Saudiyya, sakamakon batun zargin mahukuntan kasar da kisan Jamal Khashoggi.
-
Wani Dalibi Ya Kashe Dalibai 17 A Cikin Wata Makarantar Koyar Da Sana'o'i A Kasar Rasha
Oct 17, 2018 15:25Rundunar 'yan sandan kasar Rasha ta sanar da cewa: Wani dalibi dan shekaru 18 a duniya ya bude wutan bindiga kan dalibai a cikin makarantar koyar da sana'o'i inda ya kashe dalibai 17 tare da jikkata wasu 40 na daban.
-
Pompeo Na Ganawa Da Jami'an Turkiya Kan zargin Kisan Khashoggi
Oct 17, 2018 08:49Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya isa birnin Ankara na kasar Turkiya, domin ganawa da jami'an gwamnatin kasar ta Turkiya kan zargin kashe Jamal Khashoggi.
-
Kasar Venezuella Ta Soke Amfani Da Dalar Amurka
Oct 17, 2018 02:58mataimakin shugaban kasar ta Venezuella Tareck El Aissami ne ya sanar da sabon matakin na daina amfani da kudin Amurka a mu'alar cinikayya da kasashen waje
-
Macron ya yi wa Ministocinsa garanbawul
Oct 16, 2018 15:39Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya sanar da nadin sabbin ministocin ayyukan cikin gida da Noma da kuma Al'adu bayan shafe makonni yana laluben kwararrun da zai ci gaba da gudanar da aiki da su a kasar.
-
Ana Ci Gaba Da Kaiwa Musulmi Hari A Birtaniya
Oct 16, 2018 15:38Alkaluman da Ma'aikatan Cikin gidan Birtaniya ta fitar ya nuna cewa masu gyamar addinin musulmi a kasar na karuwa.
-
Ambaliyar Ruwa Ta Kashe Mutum Akalla 13 A Faransa
Oct 15, 2018 14:15Ruwan sama tamakar da bakin kwarya da suka haifar da ambaliya sun yi sanadin mutuwar mutum akalla 13 a yankin kudu maso yammacin Faransa.
-
Amurka : Trump Ya Ce Mai Yiyuwa Kashe Kashoggi Akayi
Oct 15, 2018 11:59Shugaba Donald Trump na Amurka ya ce mai yiyuwa ne an kashe dan jaridan nan ne na Saudiyya Jamal Khashoggi.
-
Erdogan Da Salman Sun Tattauna Ta Wayar Tarho kan Kashoggi
Oct 15, 2018 02:55Shugabannin Saudiyya da Turkiyya sun tattauna ta wayar tarho kan batan dan jarida Jamal Khashoggi da ake zargin an kashe shi a karamin ofishin jakadancin Saudiyar na Istambul a farkon watan nan.
-
Hatsarin Jirgin Sama Ya Ci Rayukan Mutum 3 A Yammacin Jamus
Oct 15, 2018 02:52Wani karamin jirgin sama ya fadi cikin mutane a jahar Hesse na kasar Jamus, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutum 3 da kuma jikkata wasu takwas na daban