Macron ya yi wa Ministocinsa garanbawul
(last modified Tue, 16 Oct 2018 19:09:34 GMT )
Oct 16, 2018 19:09 UTC
  • Macron ya yi wa Ministocinsa garanbawul

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya sanar da nadin sabbin ministocin ayyukan cikin gida da Noma da kuma Al'adu bayan shafe makonni yana laluben kwararrun da zai ci gaba da gudanar da aiki da su a kasar.

Kamfanin dillancin labaran kasar ya habarta cewa a wannan talata Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya yi garambawul a Majalisar Ministocinsa, in da ya nada shugaban Jam’iyyarsa mai mulki, Christophe Castaner a matsayin sabon Ministan Cikin Gida.

Ana kallon garambawul din a matsayin wani yunkurin Macron na karfafa gwamnatinsa bayan wasu tsoffin ministocinsa da suka hada da na Cikin Gida, Gerard Collomb da na Muhalli, Nicolas Hulot sun yi murabus.

Ministan Kudi, Bruno Le Maire da Ministan Harkokin Waje, Jean Yves Le Drien za su ci gaba da rike mukamansu, yayin da a gefe guda aka nada sabbin Ministocin Noma da na Raya Al’adu.

Kimanin mako guda kenan da ake dakon matakin Macron na garambawul a Majalisar Ministocin nasa.

A baya bayan nan dai farin jinin Shugaba Macron ya ragu sakamakon jinkiri wajen daukar matakan gaggawa kan matsalolin tattalin arziki a kasar.