Hatsarin Jirgin Sama Ya Ci Rayukan Mutum 3 A Yammacin Jamus
https://parstoday.ir/ha/news/world-i33629-hatsarin_jirgin_sama_ya_ci_rayukan_mutum_3_a_yammacin_jamus
Wani karamin jirgin sama ya fadi cikin mutane a jahar Hesse na kasar Jamus, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutum 3 da kuma jikkata wasu takwas na daban
(last modified 2018-10-15T02:52:02+00:00 )
Oct 15, 2018 02:52 UTC
  • Hatsarin Jirgin Sama Ya Ci Rayukan Mutum 3 A Yammacin Jamus

Wani karamin jirgin sama ya fadi cikin mutane a jahar Hesse na kasar Jamus, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutum 3 da kuma jikkata wasu takwas na daban

Kamfanin dillancin labaran Irna ya nakalto jami'an 'yan sandar kasar Jamus na cewa a marecen jiya Lahari wani karamin jirgi ya yi hatsarin a yayin da yake kokarin tashi,a kusa da garin fulda na yammacin kasar,  inda ya fada cikin taron ja'ama.

Sanarwar jami'an 'yan sandar Jamus din ta ce, hatsarin ya yi sanadiyar mutuwar mutum uku cikinsu kuwa harda yaro karami, sannan wasu takwas na daban sun jikkata, inda tuni aka garzaya da su zuwa asibiti, inda suke karbar magani a can.

Har yanzu dai ba a bayyana dalilin wannan hatsarin ba, saidai tuni aka ci gaba da gudanar da bincike domin gano musababin hatsarin.