Ambaliyar Ruwa Ta Kashe Mutum Akalla 13 A Faransa
(last modified Mon, 15 Oct 2018 17:45:07 GMT )
Oct 15, 2018 17:45 UTC
  • Ambaliyar Ruwa Ta Kashe Mutum  Akalla 13 A Faransa

Ruwan sama tamakar da bakin kwarya da suka haifar da ambaliya sun yi sanadin mutuwar mutum akalla 13 a yankin kudu maso yammacin Faransa.

bayanai sun nuna cewa ruwan wata uku ne aka tafka a cikin 'yan sa'o'i a cikin daren jiya Lahadi a lardin Aude, lamarin da ya haifar da ambaliya data yi janyo hasara rayukan mutane akalla 13.

Ko baya ga hakan ruwan sun haifar da barna mai yawa, wacce ta kai ga katsewar wutar lantarki a gidaje kimanin 8 000 na lardin.

Tuni dai aka aike da jmai'an ceto a yankin don agazawa jama'a duk da cewa ana cikin fargaba dangane da yanayi.

Hukumomin Kasar sun ce ba'a taba ganin irin wannan ambaliyar ruwa mai muni kamar haka ba a cikin tsawan shekaru da dama a kasar.

Fadar Shugaban kasar ta sanar da cewa shugaba Emmanuel Macron zai ziyarci yankin a yayinda tuni Firaministan Kasar, Edouard Philippe ya isa yankin na Aude domin jajantawa jama'a.