Kasar Venezuella Ta Soke Amfani Da Dalar Amurka
https://parstoday.ir/ha/news/world-i33662-kasar_venezuella_ta_soke_amfani_da_dalar_amurka
mataimakin shugaban kasar ta Venezuella Tareck El Aissami ne ya sanar da sabon matakin na daina amfani da kudin Amurka a mu'alar cinikayya da kasashen waje
(last modified 2018-10-17T06:28:10+00:00 )
Oct 17, 2018 06:28 UTC
  • Kasar Venezuella Ta Soke Amfani Da Dalar Amurka

mataimakin shugaban kasar ta Venezuella Tareck El Aissami ne ya sanar da sabon matakin na daina amfani da kudin Amurka a mu'alar cinikayya da kasashen waje

El Aissami ya ci gaba da cewa; kasar Venezuella za ta maye gurbin dalar Amurka da kudin kasashen turai, Euro da kuma wasu kudaden masu daraja na duniya.

Mataimakin shugaban kasar ta Venezuella ya kuma ce; ba da jimawa ba gwamnati za ta zuba euro biliyan biyu a cikin kasuwannin kudaden na aksar.

Kasar Amurka dai tana amfani da kudinta na dala a matsayin wani makamin  matsin lamba akan kasashen da ba ta ga maciji da su.

A cikin watannin bayan nan kasar ta Venezuella ta fuskanci tashe-tashen hanakli da 'yan hamayyar siyasa suke jagoranta. Kasar Amurka da kawayenta a yankin suna kokarin kifar da gwamnatin Nichols Maduro ta hanayr taimakawa 'yan hamayya da kuma kakaba takunkumai akan gwmanatin kasar.