Oct 18, 2018 05:52 UTC
  • Ministan Harkokin Wajen Jamus Ya Jingine Batun Tafiyarsa Zuwa Saudiyya

Ministan harkokin wajen kasar Jamus Heiko Maas ya dakatar da tafiyar da aka shirya cewa zai zuwa kasar Saudiyya, sakamakon batun zargin mahukuntan kasar da kisan Jamal Khashoggi.

Tashar talabijin ta Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, Jamus ta jingine batun ziyarar da ministan harkokin wajen kasar zai kaia  kasar Saudiyya, har zuwa lokacin da za  afitar da sakamakon bincike kan zargin kisan Khashoggi, inda  a lokacin ne Jamus din za ta yanke shawara kan batun ziyarar.

A nata bangaren kungiyar tarayyar turai ta gargadi gwamnatin Saudiyya da cewa, matukar dai har ta tabbata cewa mahukuntan kasar suna da hannu a cikin abin da ya faru da Khashoggi, to kuwa lallai tarayyar turai za ta dauki matakin ba sani ba sabo wajen ladabtar da gwamnatin kasar ta Saudiyya.

Yayin da shi kuma a nasa bangaren shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa, ba ya son ya samu rashin jituwa tsakaninsa da Saudiyya saboda batun Khashoggi, domin kuwa yanzu haka Saudiyya ta kulla wani cinikin makamai wanda za ta saya daga Amurka da ya kai dala biliyan 110.

 

Tags