Pars Today
Shugabar kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya ta gargadi India kan cutar da musulmi.
Gwamnatin Shugaba Nicolas maduro na kasar Venezuela ta sanar da korar jakadan kasar Jamus, daga kasar.
An kiyasta cewa yan Najeriya kimani 1863 suka bace a cikin kasar Rasha bayan shigarsu kasar a matsayin masu karfafa guiwar yan wasan Nigeriya.
Hukumar kare hakkin bil adama ta Majalisar Dinkin Duniya, ta bukaci mahukuntan Faransa dasu gudanar da bincike kan amfani da karfi na jami'an 'yan sanda kan masu zanga zanga a kasar da ake kira da masu ''dorawa riga''.
John Bolton, mai bawa shugaban kasar Amurka shawara kan al-amuran tsaro ya yi barazanar cewa dole ne Korea ta Arewa ta wargaza shirinta na makaman nukliya ko kuma Amurka ta kara dora mata wasu sabbin takunkuman tattalin arziki.
Sakataren harkokin wajen Amurka ne ya sanar da cewa; Nan da wani lokaci Amurkan za ta aike da jami’an diplomsiyya zuwa kasar Korea Ta Arewa domin cigaba da tattaunawa
A jiya Litinin ne shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanya hannu akan tsawaita takunkumin kasar kasar Zimbabwe saboda abin da ya kira ci gaba da yi wa manufofin Amurka barazana da take yi.
A dai-dai lokacinda rikicin kasar Veneziela ke kara tsanani , daruruwan mutanen kasar sun fara tsallakawa zuwa kasashe makobta.
Kamfanin dillancin labarun Sputnik na kasar Rasha ya ba da labarin cewa A jiya Litinin ce sojojin kasar Indiya su ka harbo jirgi maras matuki na kasar Pakistan a ci gaba da yakin da kasashen biyu suke fafatawa