-
Jami'an Tsaron Somaliya Sun Hallaka 'Yan Ta'addan Al-Shabab Guda 60
Mar 18, 2016 14:19Jami'an tsaro a yankin Puntland mai kwarya kwaryar cin gashin kai a kasar Somaliya sun sanar da samun nasarar hallaka wasu 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Al-Shabab su 60 a wani harin da suka kai musu da ya ba su damar kwace wasu yankuna da 'yan ta'addan suke rike da su.
-
Shugaban Kongo Na Kokarin Ta Zarce, 'Yan Adawa Na Zarginsa Da Magudi
Mar 18, 2016 13:13Shugaban kasar Kongo Sassou Nguesso na shirin sake ci gaba da shugabanci kasar a zaben jin ra'ayin al'ummar kasar da za ta gudanar a jibi Lahadi inda yake fatan al'ummar kasar za su ba shi da damar ci gaba da mulkinsa na shekaru 32 a kasar lamarin da 'yan adawa suka yi watsi da shi suna zarginsa da kokarin murguda sakamakon zaben.
-
Guinea : An Gano Wasu Mutane Biyu Dauke Da Ebola
Mar 18, 2016 06:43Rahotanni daga kasar Guinea na cewa an samu wasu mutane biyu dauke da cutar Ebola bayan gwajin da aka musu sanadin bayyana alamun cutar.
-
Al-Qaida Ta Ce Ta Kai Hari Ivory Coast Don Daukar Fansa Kan Faransa
Mar 16, 2016 13:55Kungiyar Al-Qa'ida reshen arewacin Afirka ta sanar da cewa ta kai hari kasar Ivory Coast ne don daukar fansa kan hare-haren da sojojin Faransa suke kai wa 'ya'yanta a yankin Sahel tana mai kiran sojojin Faransa da su fice daga wannan yankin.
-
Angola : Cutar Shawara Ta Kashe Mutane 250
Mar 16, 2016 08:51A Angola mutane 250 aka rawaito cewa sun mutu sanadin cutar shawara tun bayan barkewar ta a watan Disamba da ya gabata.
-
Tarayyar Afirka Ta Yi Allah Wadai Da Harin Ta'addancin Ivory Coast
Mar 14, 2016 13:55Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta yi Allah wadai da harin ta'addancin da aka kai wani Otel a kasar Ivory Coast a jiya kamar yadda ta sanar da ta'aziyya da kuma aihininta ga gwamnati da kuma al'ummar kasar da sauran wadanda abin ya shafa.
-
Ivory Coast : AQMI Ta Dau Alhakin Kai Harin Grand Bassam
Mar 14, 2016 02:59Kungiyar 'yan ta'adan Al'Qaida reshen kasashen larabawa (AQMI) ta dau alhakin kai a wurin shakatawa nan na gabar kogi Grand Bassam a kasar Ivory Coast /Cote d'ivoire da yayi sanadin mutuwar mutane da dama.
-
Shugaban Angola Ya Ce Zai Sauka Daga Karagar Mulkin Kasar
Mar 12, 2016 05:26Shugaban kasar Angola Jose Eduardo dos Santos ya sanar da cewa ya kuduri aniyar sauka daga karagar mulkin kasar a shekara ta 2018 lokacin da wa'adin mulkinsa zai kare bayan ya shafae kusan shekaru 40 yana mulkin kasar.
-
Shugaban Angola Ya Bayyana Rashin Aniyarsa Ta Yin Tazarce A Kan Mulkin Kasar
Mar 11, 2016 14:52Shugaban kasar Angola ya sanar da aniyarsa ta rashin yin tazarce a kan karagar mulkin kasar bayan kawo karshen wa'adin mulkinsa a shekara ta 2018.
-
Zaben Shugaban Kasar Chadi
Mar 08, 2016 09:09"Yan takara 14 ne za su yi gogayya da juna a zaben shugabar kasar Chadi.