Guinea : An Gano Wasu Mutane Biyu Dauke Da Ebola
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i2611-guinea_an_gano_wasu_mutane_biyu_dauke_da_ebola
Rahotanni daga kasar Guinea na cewa an samu wasu mutane biyu dauke da cutar Ebola bayan gwajin da aka musu sanadin bayyana alamun cutar.
(last modified 2018-08-22T06:58:00+00:00 )
Mar 18, 2016 06:43 UTC
  • Guinea : An Gano Wasu Mutane Biyu Dauke Da Ebola

Rahotanni daga kasar Guinea na cewa an samu wasu mutane biyu dauke da cutar Ebola bayan gwajin da aka musu sanadin bayyana alamun cutar.

Wannan na zuwa ne ‘yan sa’oi da hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce, babu sauran cutar a kasar Saliyo mai makwabtaka da Guinea.

Wani jami’in gwamnatin kasar ya ce, mutanen da suka kamu da cutar mazauna kauyen Korokpara ne, inda aka samu mutane uku 'yan gida daya da suka rasa rayukansu a 'yan makwannin da suka gabata bayan sun yi ta amai da gudawa.

An yi amanna cewa, cutar ta Ebola ta fara bulla ne a kasar Guinea yayin da ta kashe sama da mutane dubu 11,300 tun bayan barkewarta a shekarar 2013 a kasashen Liberia da Saliyo da Guinea.