Shugaban Angola Ya Ce Zai Sauka Daga Karagar Mulkin Kasar
Shugaban kasar Angola Jose Eduardo dos Santos ya sanar da cewa ya kuduri aniyar sauka daga karagar mulkin kasar a shekara ta 2018 lokacin da wa'adin mulkinsa zai kare bayan ya shafae kusan shekaru 40 yana mulkin kasar.
Shugaba Dos Santos ya bayyana hakan ne a jiya Jumma’a a lokacin da yake jawabi a gaban wasu kusoshin jam’iyyarsa ta MPLA mai mulki inda ya sanar da su cewa tuni ya kuduri aniyar sauka daga karagar mulkin kasar a lokacin da wa'adin mulkinsa na yanzu ya kare a shekara ta 2018.
Shugaba Dos Santos dai wanda ya dare karagar mulkin kasar Angolan a shekarar 1979, shi ne shugaba na biyu a Afirka da ya fi dadewa a karagar mulkin kasarsa bayan shugaban kasar Equatorial Guinea Teodoro Obiang Nguema.
A zaman da jam'iyya mai mulkin za ta gudanar nan gaba ne dai za'a a tattauna dangane da wanda jam'iyyar za ta tsayar a matsayin dan takaranta a zaben shugaban kasar da za a gudanar a shekara mai zuwa ta 2017.