Angola : Cutar Shawara Ta Kashe Mutane 250
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i2497-angola_cutar_shawara_ta_kashe_mutane_250
A Angola mutane 250 aka rawaito cewa sun mutu sanadin cutar shawara tun bayan barkewar ta a watan Disamba da ya gabata.
(last modified 2018-08-22T06:57:59+00:00 )
Mar 16, 2016 08:51 UTC
  • Angola : Cutar Shawara Ta Kashe Mutane 250

A Angola mutane 250 aka rawaito cewa sun mutu sanadin cutar shawara tun bayan barkewar ta a watan Disamba da ya gabata.

Bayanai sun nuna cewa cutar tafi tsanani a Luanda babban birnin kasar.

Shugaban asibitin Luanda, Mateus Campos ya ce a ranar litinin da ta gabata kawai yara 27 suka mutu daga cikin mutane 900 da ke fama da cutar.

Campos ya ce ba su da isasun ma’aikatan da za su iya kula da lafiyar masu fama da cutar.

Yanzu haka gwamnatin kasar ta kaddamar da shirin rigakafi dan dakile yaduwar cutar.