Zaben Shugaban Kasar Chadi
Mar 08, 2016 09:09 UTC
"Yan takara 14 ne za su yi gogayya da juna a zaben shugabar kasar Chadi.
Kamfanin Dillancin Labarun Faransa daga birnin Adis Ababa ya ambato cewa; Shugaba Idris Deby da kuma Saleh Kabzabo ne fitattun 'yan takarar da wannan shi ne karo na uku da za su yi gogayya da juna.
Shi dai shugaba Idris Deby ya dauki shekaru 25 akan karagar mulki, kuma a halin yanzu ya sake tsayawa takara. A shekarar 2004 ne Deby ya sauya kundin tsarin mulkin kasar da ya rushe tsayawa takarar shugabancin kasa sau biyu kacal.
A halin da ake ciki da akwai 'yan takarar shugabancin kasar su 14 da za su gogayya da juna.
A ranar 10 ga watan nan na Aprilu ne dai za a gudanar da zaben shugabancin kasar ta Chadi.
Tags