Ivory Coast : AQMI Ta Dau Alhakin Kai Harin Grand Bassam
-
jami\'an tsaro na kwashe majiyanta
Kungiyar 'yan ta'adan Al'Qaida reshen kasashen larabawa (AQMI) ta dau alhakin kai a wurin shakatawa nan na gabar kogi Grand Bassam a kasar Ivory Coast /Cote d'ivoire da yayi sanadin mutuwar mutane da dama.
Harin na jiya lahadi da wasu 'yan bindiga suka kai a cewar shugaban kasar Alhassan Ouatara da ya ziyarci wurin ya yi sanadin mutuwar fararen hula 14 da kuma sojojin kasar 2, tare da raunana wasu fararen hula 19 da kuma sojoji uku.
Rahotanni sun ce maharan sun rabu gungu biyu inda suka yi ta buda wuta kan jama'a dake wurin.
Da yake karin haske dangane da lamarin a gidan talabijin na kasar ministan cikin gida na kasar Ahmed Bakayoko ya ce maharan sun farmawa otel uku dake kusa da wurin shakatawar, kuma an yi nasara hallaka maharan guda shida.
Wurin shakatawar na Grand Bassam da ke tazarar kilomita 40 daga gabashin Abidjan babban birnin kasar shi ne wurin shakatawa mafi shahara da daukar hankalin yan yawon bude ido.