-
AU Za Ta Aika Da Masu Sa Ido Kan Shariar Daukaka Kara kan Zaben Gabon
Sep 15, 2016 01:24Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta sanar da cewa tana shirin aikewa da masu sanya ido don taimakawa Kotun Kundin Tsarin Mulki na kasar Gabon wajen dubi cikin kukan da shugaban 'yan adawar kasar Jean Ping ya shigar yana zargin shugaba Ali Bongo na kasar da magudi a zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan da ya gabata.
-
Nan Ba Da Dadewa Morocco Za Ta Sake Dawowa Cikin AU
Sep 14, 2016 06:25Majalisar dokokin kasashen Afirka ta bayyana cewa, nan ba da dadewa ba, kasar Morocco za ta sake dawowa cikin kungiyar tarayyar Afirka.
-
An Yi Nasara Dakile Annobar Zazzabin Shawara A Angola Da DRC
Sep 14, 2016 06:23Hukumar lafiya ta duniya ta sanar da cewa, an samu nasarar shawo kan annobar zazzabin shawara da ta barke a kasashen Angola da jamhuriyar demokaradiyyar Congo, sakamakon gangamin allurar riga kafin cutar da aka gudanar a kasashen biyu.
-
Musulmin kasar D-Congo sun yi kira ga gwamnatin kasar da ta tabbatar da zaman lafiya
Sep 14, 2016 02:57Kiran Musulmin Kasar D-Congo ga 'yan siyasar da su tabbatar da zaman lafiya
-
Yajin Aikin Ma'aikatan Radiyon Gunea Bissau
Sep 14, 2016 02:55Rashin biyan albashi ya jefa ma'aikatan Radiyon kasar Gunea Bissau yajin aiki.
-
Ana Jiran Kotun Kolin Kasar Gabon, Domin Amincewa Da Zaben Shugaban Kasa
Sep 14, 2016 02:51Amincewa Da Zaben Shugaban Kasa Yana Damfare Da Amincewar Kotun Koli.
-
Sabuwar Gwamnatin Kasar Zambiya Ta Kama Aiki, Bayan Rantsar Da Shugaba Lungu
Sep 13, 2016 14:18A yau ne zababben shugaban kasar Zambiya Edgar Lungu ya yi rantsuwar kama aiki a wani sabon wa'adi na shugabancin kasar lamarin da ke nufin daga yau sabuwar gwamnatin kasar ta fara aikinta kenan duk kuwa da korafe korafen da 'yan adawa suke yi.
-
Somaliya : Ana Taro Kan Dabarun Yaki Da Al'Shabab
Sep 13, 2016 06:42A wani mataki mai nufin lalubo hanyoyin kara karfin yakar mayakan Al-Shabaab, sojoji injiniya daga MDD da kungiyar tarayyar Afirka(AU) na wani taron karawa juna sani a birnin Mogadisho na kasar Somaliya.
-
Somaliya : An Damke Masu Hadawa Al-Shabaab Bama bamai
Sep 12, 2016 05:04Dakarun kiyaye zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afrika dake Somaliya (AMISOM), wadanda ke samun tallafin dakarun kasar Somalia, sun cafke wasu mutane biyu da suka kware wajen hadawa kungiyar Al-Shabaab bama bamai a kudancin kasar.
-
Mutane Gabon Na Ci Gaba Da Nuna Rashin Amincewa Da Rikicin Siyasa A Kasar
Sep 11, 2016 01:26Rahotanni daga kasar Gabon sun bayyana cewar daruruwan mutanen kasar sun gudanar da wata zanga-zanga don nuna rashin amincewarsu da ci gaba da rikicin siyasa da ke faruwa a kasar bayan sanar da sakamakon shugaban kasar da aka yi.