An Yi Nasara Dakile Annobar Zazzabin Shawara A Angola Da DRC
Hukumar lafiya ta duniya ta sanar da cewa, an samu nasarar shawo kan annobar zazzabin shawara da ta barke a kasashen Angola da jamhuriyar demokaradiyyar Congo, sakamakon gangamin allurar riga kafin cutar da aka gudanar a kasashen biyu.
Daraktan kula da yaki da annoba na hukumar ta WHO / OMS, Sylvie Briand, ya bayyana a taron manema labarai cewa a halin yanzu an shawo kan wannan annoba, kuma ba'a samu rahoton wanda ya sake kamuwa da cutar ba a wadannan kasashen biyu ba.
A 'yan kwanakin nan, an gudanar da gangamin alluran rigakafin cutar ne da nufin dakile yaduwar kwayoyin cutar, to sai dai babban abin da ake fargaba shi ne, yadda za'a hana kwayoyin cutar sake bazuwa a nan gaba, musamman a lokacin farkon damina.