Somaliya : An Damke Masu Hadawa Al-Shabaab Bama bamai
Dakarun kiyaye zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afrika dake Somaliya (AMISOM), wadanda ke samun tallafin dakarun kasar Somalia, sun cafke wasu mutane biyu da suka kware wajen hadawa kungiyar Al-Shabaab bama bamai a kudancin kasar.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke shirye shiryen karbar bakuncin taron koli na kasashen shiyyar gabashin Afrika, wanda za'a gudanar a gobe Talata.
Dakarun na hadin gwiwa sun ce, sun samu nasarar damke masana hada boma boman ne a lokacin da suke ci gaba da yin sintiri a yankin Lower Juba, dake kudancin birnin Kismayo..
Tuni dai aka girke jami'an tsaro masu yawan gaske a fadin kasar, musamman babban birnin kasar Mogadishu domin tabbatar da tsaro, domin kaucewa duk wata barazana da zata iya kunno kai a yayin taron mai cike da mahimmaci.