Nan Ba Da Dadewa Morocco Za Ta Sake Dawowa Cikin AU
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i11035-nan_ba_da_dadewa_morocco_za_ta_sake_dawowa_cikin_au
Majalisar dokokin kasashen Afirka ta bayyana cewa, nan ba da dadewa ba, kasar Morocco za ta sake dawowa cikin kungiyar tarayyar Afirka.
(last modified 2018-08-22T06:58:55+00:00 )
Sep 14, 2016 06:25 UTC
  • Nan Ba Da Dadewa Morocco Za Ta Sake Dawowa Cikin AU

Majalisar dokokin kasashen Afirka ta bayyana cewa, nan ba da dadewa ba, kasar Morocco za ta sake dawowa cikin kungiyar tarayyar Afirka.

Mai magana da yawun majalisar dokokin kasashen Afirka Roger Nkodo Dang ya shaidawa wani taron manema labarai bayan ganawarsa da takwaransa na majalisar wakilan kasar Morocco Rachid Talbi Alami cewa, majalisar dokokin kasashen Afirka za ta taka rawar da ta dace wajen ganin ta hade kan nahiyar wuri guda. 

Tun a shekarar 1984, lokacin da ake kiran kungiyar da suna, kungiyar hada kan kasashen Afirka ne dai kasar ta Morocco ta fice daga cikin kungiyar. Kana a watan Yuli, Moroccon ta sanar da cewa, za ta sake dawowa cikin kungiyar tarayyar Afirka, shekaru 32 bayan ficewarta.