Sabuwar Gwamnatin Kasar Zambiya Ta Kama Aiki, Bayan Rantsar Da Shugaba Lungu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i10999-sabuwar_gwamnatin_kasar_zambiya_ta_kama_aiki_bayan_rantsar_da_shugaba_lungu
A yau ne zababben shugaban kasar Zambiya Edgar Lungu ya yi rantsuwar kama aiki a wani sabon wa'adi na shugabancin kasar lamarin da ke nufin daga yau sabuwar gwamnatin kasar ta fara aikinta kenan duk kuwa da korafe korafen da 'yan adawa suke yi.
(last modified 2018-08-22T06:58:55+00:00 )
Sep 13, 2016 14:18 UTC
  • Sabuwar Gwamnatin Kasar Zambiya Ta Kama Aiki, Bayan Rantsar Da Shugaba Lungu

A yau ne zababben shugaban kasar Zambiya Edgar Lungu ya yi rantsuwar kama aiki a wani sabon wa'adi na shugabancin kasar lamarin da ke nufin daga yau sabuwar gwamnatin kasar ta fara aikinta kenan duk kuwa da korafe korafen da 'yan adawa suke yi.

Rahotanni daga kasar Zambiyan sun bayyana cewar an gudanar da bikin rantsuwar da kuma kama aikin ne bayan da kotun koli ta kasar ta yi watsi da kiran da madugun 'yan adawar kasar Hakainde Hichelima na a dakatar da rantsar da shugaba Lungun a matsayin sabon shugaban kasar saboda zargin da yake yi na an tabka magudin zabe.

Rahotannin sun ce tun da safiyar yau ne dai aka rantsar da shugaba Lungun da mataimakinsa a wa'ni sabon wa'adin mulki, inda sabon shugaban ya kirayi 'yan kasar da su zauna lafiya ya kuma yi alkawarin ci gaba da aiki tukuru wajen tabbatar da ci gaban kasar.

Bikin na yau dai ya sami halartar baki 'yan kasashen waje da suka hada da shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe, shugaban Uganda Yoweri Museveni, shugaban kasar Botswana Ian Khama, da shugaban kasar Tanzaniya John Magufuli , sai kuma mataimakin shugaban kasar Kenya William Ruto.