Ana Jiran Kotun Kolin Kasar Gabon, Domin Amincewa Da Zaben Shugaban Kasa
Amincewa Da Zaben Shugaban Kasa Yana Damfare Da Amincewar Kotun Koli.
Amincewa Da Zaben Shugaban Kasa Yana Damfare Da Amincewar Kotun Koli.
Cibiyar Labaru ta "Afirca Times" ta ambaci cewa; Dan takarar shugaban kasar da bai yi nasara ba, Jean Ping ne ya bijiro ba batun sakamakon zaben a gaban kotun kolin kasar.
Gwamantin kasar ta Gabon a karkashin shugaban kasa Ali Bongo, ta yi suka akan shigar da karar Jean Ping, domin ta yi imani da cewa babu wani magudi a cikin zaben.
A makon da ya gabata ne dai hukumar zaben kasar ta sanar da Ali Bango a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar.
Magoya bayan Jean Ping sun bazama kan titunan birnin Libreville domin nuna kin amincewarsu da samakamon zaben.