-
Gwamnatin Masar Ta Jaddada Matsayinta Na Taimakawa Iraqi Kan Yaki Da Ta'addanci
Oct 23, 2017 06:25Shugaban kasar Masar Abdulfatah Sisi ya kara jaddada matsayin gwamnatinsa na tallafa wa kasar Iraqi a yakin da take yi da yan ta'adda.
-
Iraki: Babbar Jam'iyyar Adawa A Yankin Kurdistan Ta Bukaci A Kafa Gwamnatin Tseratar Da Mutanen Yankin
Oct 23, 2017 06:25Jam'iyyar adawa mafi girma a yankin kursdistan na kasar Iraqi ta bukaci Massoud Barazani ya sauka daga kujerar shugabancin yankin sannan a kafa gwamnatin tseratar da yakin daga halin da Barazani ya jefa shi a ciki.
-
Ayat. Sistani Ya Bukaci Gwamnati Da Ta Kare Kurdawan Iraki Duk Kuwa Da Sabanin Da Ake Da Shi
Oct 20, 2017 17:17Babban marja'in 'yan Shi'an kasar Iraki, Ayatullah Sayyid Ali Sistani ya kirayi gwamnatin kasar Irakin da ta ba wa Kurdawan kasar kariya duk kuwa da sabanin da ya kunno kai da kuma ci gaba da kai ruwa rana da ake yi tsakanin gwamnatin Iraki da na yankin Kurdawan da suke son ballewa.
-
Sojoji Sun Shiga birnin Sinjar Da Ke Arewacin Iraki
Oct 17, 2017 12:32Da safiyar yau ne dai sojojin na Iraki suka kutsa garin na Sinjar bayan da mayakan kurdawa na Peshmarga suka janye daga cikinsa.
-
Dakarun Iraki Sun Kwato Garin Kirkuk
Oct 17, 2017 05:51Dakarun Iraki sun kwato garin Kirkuk ciki har da wasu mahimman wurare da suka hada da ofishin gwamnan lardin da sansanin soji da cibiyoyin mai da kuma filin jirgin sama.
-
Iraki : Kasancewar Mayakan PKK A Kirkuk Shelanta Yaki Ne
Oct 15, 2017 17:43Gwamnatin Iraki ta ce kasancewar mayakan kurdawa Turkiyya na PKK a yankin Kirkuk da sojojin kasar ke kokarin kwatowa shelanta yaki ne a kan ta.
-
Iraki : Kotu Ta Umurci A Cafke Wadanda Suka Shirya Zaben Kurdistan
Oct 11, 2017 16:53Wata kotu a Iraki ta bada umurnin a cafke mutanen da suka jagoranci shirya zaben raba gardama na bellewar yankin Kurdistan.
-
Iraki: "Rasul Ali" Zai Zama Magajin Jalal Talibani A Jam'iyyar "PUK"
Oct 08, 2017 08:21Wani jami'i a jam'iyyar "Patriotic Union of Kurdistan" Giyath al-Surjy, ya ce; Kosrat Rasul Ali ne zai maye gurbin Jalal Talibani a shugabancin jam'iyyar.
-
Iraki / Kurdistan : Ba Ma Son Yin Fito Na Fito _Abadi
Oct 05, 2017 10:06Firayi ministan Iraki Haider al-Abadi ya tabbatar da cewa ba sa son yin fito na fito bayan zaban raba gardama yankin Kurdistan.
-
Dakarun Iraki Sun Kutsa Kai A Birnin Hawija
Oct 04, 2017 10:58Majiyoyin soji a Iraki sun ce dakarun hadin gwiwa na kasar sun kutsa kai a birnin Hawija, sansani na karshe na 'yan ta'addan kungiyar (IS) a arewacin kasar.