Sojoji Sun Shiga birnin Sinjar Da Ke Arewacin Iraki
Da safiyar yau ne dai sojojin na Iraki suka kutsa garin na Sinjar bayan da mayakan kurdawa na Peshmarga suka janye daga cikinsa.
Dama tun jiya talata ne dai sojojin Irakin suka kwace iko da garin Karkuku da ake da sabani akansa a tsakanin Bagadaza da Arbil. Pira ministan kasar Haydar Abadi ya bai wa sojojin kasar umarnin da su kare rayuka da dukiyar mazauna birnin.
'Yan sandan birnin Karkuk sun sanar da cewa da cewa za su bude ayyukansu daga mako mai zuwa. Gabanin shigar sojojin na Iraki, kurdawan da su ke iko da shi, sun dakatar da aikin gwamnati da suka hada da na jami'an tsaro.
Sabanin da ya kunno kai a tsakanin jam'iyyun kurdawa biyu dangane da kwacewar da birnin Karkuk ya yi daga hannunsu, ya sa suna zargin juna da ha'inci.
Yarjejeniyar raba gardama akan ballewar yankin na kurdawa ne ya jawo zaman dardar a kasar ta Iraki da ma yankin gabas ta tsakiya.