Iraki : Kasancewar Mayakan PKK A Kirkuk Shelanta Yaki Ne
(last modified Sun, 15 Oct 2017 17:43:45 GMT )
Oct 15, 2017 17:43 UTC
  • Iraki : Kasancewar Mayakan PKK A Kirkuk Shelanta Yaki Ne

Gwamnatin Iraki ta ce kasancewar mayakan kurdawa Turkiyya na PKK a yankin Kirkuk da sojojin kasar ke kokarin kwatowa shelanta yaki ne a kan ta.

Wata sanarwa da kwamitin tsaro da firayi ministan kasar Haider al-Abadi ya jagoranta ta ce babban hadari ne kana kuma shelanta yaki ne kasancewar mayakan da basu cikin rundinar tsaro ta yankin na Kirkuk wanda suka hada da mayakan Kurdawa na PKK wanda Turkiyya da Amurka ke dangantawa da 'yan ta'adda.

Gwamnatin ta ce ba zata iya rufe ido ba akan shelanta ma 'yan kasar da dakarun gwamnati yaki ba, don haka dakarun kasar zasu sauke nauyin da ya rataya a kansu na kare al'ummar kasar da martabarta da kuma hadin kan ta.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da sabon wa'addin da aka baiwa sojojin Kurdawan 'yan peshmergas na su janye daga yankin na Kirkuk mai arzikin man fetur wanda suka shinfida ikonsu a lokacin da aka shiga yaki da 'yan ta'addan IS a 2014.

Kawo yanzu dai duk wani yunkuri na tattaunawa tsakanin bangarorin biyu ya cutura, inda shugabannin Kurdawa suka yi kunnan uwar shegu akan kiraye kirayen gwamnatin Bagadaza na su janye dakarunsu da kuma soke zaben raba gardama da aka gudanar kan ballewar yankin kafin a shiga wata tattaunawa.