Iraki : Kotu Ta Umurci A Cafke Wadanda Suka Shirya Zaben Kurdistan
Wata kotu a Iraki ta bada umurnin a cafke mutanen da suka jagoranci shirya zaben raba gardama na bellewar yankin Kurdistan.
Mutanen da umurnin ya shafa sun hada da shugaba da kuma mambobi biyu na kwamitin da ya shiya zaben, kamar yadda kakakin majalisar koli ta shiri'a a kasar ta Iraki Abdel Sattar al-Bireqdar ya shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP.
Wannan matakin dai ya biyo bayan da majalisar tsaron kasar da firayi ministan Irakin Haider al-Abadi ya mika batun ga kotun kasar.
Kotun ta ce Hendren Saleh shugaban kwamitin da Yari Hadji Omar Da kuma Wahida Yofo Hermer sun shirya zaben gardama duk da haramcin kotun kolin kasar na gudanar da shi.
Matakin dai ya zo ne makwanni biyu bayan zaben raba gardama da ya samu amuncewa da gagarimun rinjaye daga al'ummar Kurdistan kans smarwa da yancin yancin kai.
A ranar Litini da ta gabata gwamnatin Iraki ta kara tsauraren matakan maida martani ga gwamnatin Kurdistan da suka hada dana kasuwanci da kuma shari'a aman ba tare da fayyace su matakan ba.