Dakarun Iraki Sun Kwato Garin Kirkuk
Dakarun Iraki sun kwato garin Kirkuk ciki har da wasu mahimman wurare da suka hada da ofishin gwamnan lardin da sansanin soji da cibiyoyin mai da kuma filin jirgin sama.
Bayanai daga kasar dai sun ce da yammacin jiya Litinin, dakarun sun cimma gurinsu a yankin da ake takadamma tsakanin gwamnatin Iraki da kuma kurdawan da suka jefa kuri’ar ballewa daga kasar.
Daga tutar Iraki gaban ofishin gwamnan Kirkuk maimakon ta Kurdawa na nufin gwamnatin Bagadaza ta karbi ikon lardin mai arzikin man fetur.
Dama kafin hakan gwamnatin Bagadaza ta tsige gwamnan lardin na Kirkuk, Najm Eddine Karim, saboda goyan bayan zaben raba gardama na yankin Kurdistan.
A halin da ake ciki kasashen duniya na ci gaba da kiran a kai zuciya nesa, ka da rikicin ya maida hannun agogo baya a yakin da ake da 'yan ta'addan dake kokarin shinfida ikonsu a yankin.