Pars Today
Majiyar tsaro daga kasar ta Kamaru ta ce 'yan tawaye masu magana da harshen turanci ne su ka kai harin wanda ya jikkata soja guda sannan kuma wasu biyar su ka bace.
Kamfanin dillancin labaran Anatoli na Turkiya ya ce baya ga sojojin gwamnatin Kamaru biyu da 'yan awaren su ka kashe, wasu karin 50 sun sami raunuka.
Jami'an tsaro a birnin yahunde na kasar Kamaru sun bude wuta kan wasu yan bindiga da suka kai hari kan gidan sakatarin gwamnatin kasar Mr Ferdinand Ngoh Ngoh a daren asabar da ta gabata.
A Jamhuriya Kamaru, a kalla mutane 11 ne suka rasa rayukansu, ciki har da sojoji 5, a wani rikici a yankin masu magana da turancin Ingilishi a arewa maso gabashin kasar.
A Jamhuriya Kamaru, wasu mutane da ake danganta wa da 'yan fafatukar a ware a yankin masu magana da turancin Ingilishi sun kubutar da fursuna 163 a wani gidan kurkukun yankin.
A Kamaru, an fitar da jerin sunayen 'yan takara 28 dake neman fafata wa a zaben shugaban kasar na ranar 7 ga watan Oktoba mai zuwa.
Rahotanni daga Kamaru, na cewa an cafke wasu sojojin kasar hudu, sakamakon wani hoton bidiyo dake yawo a shafukan sada zumunta, inda ana nuna wasu jami'an tsaro sun hallaka wasu mata cikin har da wata mai goyo.
Shugaban kwamitin kungiyar tarayya Afrika ta (AU), Musa Faki Mahamat, ya fara wata ziyara yau Alhamis, a Jamhuriya Kamaru, inda kuma zai gana da shugaban kasar, Paul Biya, kamar yadda fadar shugaban kasar Kamarun ta sanar.
A Jamhuriya Kamaru, an tsaida ranar 7 ga watan Oktoba mai zuwa na shekarar nan ta 2018, a matsayin ranar zaben shugaban kasa, kamar yadda aka sanar a gidan talabijin din kasar CRTV.
Wasu masu dauke da makamai ne su ka kai hari akan 'yan sanda masu sintiri a yankin na masu magana da harshen turanci ingilishi wanda ya kashe mutane 4