Yan Bindiga Sun Kai Hari Kan Gidan Sakatarin Gwamnatin Kasar Kamaru
(last modified Mon, 13 Aug 2018 19:10:57 GMT )
Aug 13, 2018 19:10 UTC
  • Yan Bindiga Sun Kai Hari Kan Gidan Sakatarin Gwamnatin  Kasar Kamaru

Jami'an tsaro a birnin yahunde na kasar Kamaru sun bude wuta kan wasu yan bindiga da suka kai hari kan gidan sakatarin gwamnatin kasar Mr Ferdinand Ngoh Ngoh a daren asabar da ta gabata.

Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ta nakalto wasu jiridun kasar kamaru dauke da wannan labarun sun kuma kara da cewa an kashe wadanda suka kawo harin guda biyu sannan an kama wasu ukku a yayinsa wasu kuma suka tsare da raunuka a jikinsu.

Labarin bai bayyana ko sakataren gwamnatin yana gidansa a lokacin da aka kaiwa gidansa harinba. Masana suna ganin hare haren ba zasu rasa nasaba da tawayen da mutanen yankin da suke magana ha harshen ingilishi suke yi ba. 

Banda haka shugaban kasar Paul Biya wanda ya dare kan kujerar shugabancin kasar tun ranar  6 ga watan Nuwamban 1982 ya sake tsayawa takarar shugabancin kasar wanda za'a gudanar a cikin watan Octoban shekarar da muke ciki..