"Yan Tawaye Sun Kai Hari A Arewacin Kasar Kamaru
Majiyar tsaro daga kasar ta Kamaru ta ce 'yan tawaye masu magana da harshen turanci ne su ka kai harin wanda ya jikkata soja guda sannan kuma wasu biyar su ka bace.
Kamfanin dillancin labarun Faransa ya ce; "Yan tawayen sun kai hari ne a wata makaranta da take gartin Bafut a yankin arewa maso yammacin kasar.
Rahotanninn farko sun ambaci cewa sojoji 8 ne su ka bace, sai dai an saki uku daga cikinsu daga baya.
Yankunan da suke magana da harshen Ingilishi a kasar ta Kamaru da suka hada gundumomin arewa maso yamma da kuma kudu maso yamma, sun fara daukar makamai ne a shekarar da ta gabata ta 2017.
Mazauna yankunan suna zargin gwamnatin kasar da nuna musu wariya bisa dalilai na harshen da suke magana da shi a yankin.
Adadin masu magana da harshen na Ingilishi a yankunan biyu sun kai kaso 20 % na jumillar mutanen kasar miliyan 20.