Ana Tsare Da Wasu Sojoji, Bayan Nuna Wani Bidiyo Na Kisan Kai
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i32403-ana_tsare_da_wasu_sojoji_bayan_nuna_wani_bidiyo_na_kisan_kai
Rahotanni daga Kamaru, na cewa an cafke wasu sojojin kasar hudu, sakamakon wani hoton bidiyo dake yawo a shafukan sada zumunta, inda ana nuna wasu jami'an tsaro sun hallaka wasu mata cikin har da wata mai goyo.
(last modified 2018-08-22T11:32:08+00:00 )
Jul 20, 2018 10:29 UTC
  • Ana Tsare Da Wasu Sojoji, Bayan Nuna Wani Bidiyo Na Kisan Kai

Rahotanni daga Kamaru, na cewa an cafke wasu sojojin kasar hudu, sakamakon wani hoton bidiyo dake yawo a shafukan sada zumunta, inda ana nuna wasu jami'an tsaro sun hallaka wasu mata cikin har da wata mai goyo.

Hoton dai ya tayar da hankalin jama'a a cikin da wajen aksar ba kadan ba.

Sun dai jami'an tsaro dake cikin bidiyon na zargin matan da cewa 'yan boko haram ne.

Ana ta dai tababa akan labarin cafke sojojin, a yayin da gwamnatin Kamarun ta ki amince wa da sahihancin hoton bidiyon.