An Tsaida Ranar Zaben Shugaban Kasa A Kamaru
A Jamhuriya Kamaru, an tsaida ranar 7 ga watan Oktoba mai zuwa na shekarar nan ta 2018, a matsayin ranar zaben shugaban kasa, kamar yadda aka sanar a gidan talabijin din kasar CRTV.
A kudirin doka na shugaban kasar da aka sanar, an kirayi dukkan 'yan kasar da suka cancanci kada kuri'a da su fito zaben shugaban a ranar 7 ga watan Oktoba dake tafe.
Kawo yanzu dai an samu 'yan takara da dama da suka ajiye takardun neman takararsu a zaben, saidai har kawo yanzu shugaban kasar mai ci, Paul Biya, bai fayyace matsayarsa ba akan ko zai sake tsayawa takara ko kuma a'a.
Tun a shekara 1982 ne, shugaba Biya mai shekaru 86, ke shugabancin kasar ta Kamaru, kuma har yanzu magoya bayansa musamman daga bangaren jam'iyya mai mulki ta (RDPC), na kiransa da ya sake tsayawa takara don neman wani wa'adi na mulki na shekaru bakwai nan gaba, saidai har yanzu bai yanke shawara kan wannan kiran ba.