Kamaru : Fursuna 163 Sun Arce Daga Wani Gidan Kurkuku
A Jamhuriya Kamaru, wasu mutane da ake danganta wa da 'yan fafatukar a ware a yankin masu magana da turancin Ingilishi sun kubutar da fursuna 163 a wani gidan kurkukun yankin.
Lamarin dai ya auke ne a cikin daren ranar Asabar zuwa Lahadi, kuma daga cikin fursuna da aka kubutar har da wasu mayakan 'yan a ware da dama.
Bayanai babu wani abunda ya yi saura daga gidan kurkukun na lardin Ndop, dake yankin arewa maso yammacin kasar.
Katoman yankin ya ce mahara kimanin hamsin ne suka farma wa gidan kurkukun, kuma bayan sun kubutar da fursuna suka bamka ma gidan kurkukun man fetur tare da bamka masa wuta.
Maharan sun kuma yi ta harbi, ta yadda ko jami'an tsaro jandarma da 'yan sanda da suka so kawo dauki basu tabaka komai ba.
Ba'a dai samu hasara rayukan ba a lamarin, amma tuni jami'an tsaro suka shiga farautar fursunan.