-
Najeriya : Obasanjo Ya Sasanta Da Atiku Abubakar
Oct 11, 2018 19:03Tsohon shugaban kasar tarayyar Najeria Olusegun Obasanjo ya sasanta da Atiku Abubakar, inda ya yafe masa duk laifuffukan da ya yi masa a baya ya kuma amince da cewa zai goyi bayansa a zabe na shekara ta 2019.
-
Ma'aikatan Filin Jirgin Sama A Lagos Sun Yi Barazanar Fadada Yajin Aikin
Oct 11, 2018 19:02Kungiyar ma'aikatan tashar jiragen sama ta Murtala Mohammad a birnin Lagos a Najeria ta yi barazanar fadada yajin aikin da take yi saboda korar wasu abokan aikinsu wanda hukuma mai kula da tashar jiragen saman ta yi.
-
Boko Haram : An Kashe Sojojin Najeriya 7
Oct 11, 2018 12:20Kamfanin dillancin labarun Faransa ya ambato wata sanarwa ta sojojin Najeriya da take cewa an kashe 7 daga cikinsu akan iyakar kasar da jamhuriyar Nijar.
-
Jam'iyyar PDP Ta Zabi Atiku A Matsayin Dan Takararta A Zaben 2019
Oct 07, 2018 17:07Jam'iyyar PDP a Nijeriya ta zabi tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar a matsayin dan takararta a zaben shugaban kasar da za a gudanar a a watan Fabrairun 2019 wanda ake ganin zai zama shi ne babbar wanda zai kalubalancin shugaban kasar Muhammadu Buhari wanda shi ma jam'iyyarsa ta APC ta tsayar da shi a matsayin dan takararta.
-
Najeriya : Buhari Ya Godewa APC
Oct 07, 2018 12:00Shugaba Muhammadu Buhari na tarayyar Najeriya a jawabin da ya gabatar a taron jam'iyyarsa ta APC a Abuja a jiya da dare ya godewa yan jam'iyyar da suka amince da shi a matsayin dan takara tilo a zaben fidda gwani na dan takara shugaban kasa a karkashin tutar jam'iyyar na zaben shekara mai zuwa.
-
Najeriya : Yan Takara 12 Ke Zawarcin Shugabancin PDP
Oct 06, 2018 06:42A yau Asabar ce 6 ga watan Octoba ake saran jam'iyyar PDP, jam'iyyar adawa mafi girma a tarayyar Najeriya za ta fidda dan takara guda daga cikin mutane 12 da suke neman tikitin takarar shugabancin kasa karkashin tutar jam'iyyar a shekara mai zuwa.
-
Makarantar Kimiyya Da Fasaha Ta Nekede A Birnin Owerri Ita Ce Ta Farko A Kasa
Oct 05, 2018 06:33Hukuma mai kula da makarantun kimiya da fasaha ta najeriya ta bayyana cewa makarantar kimiya da fasaha ta Nekedi da ke birnin Owerri ita ce ta farko a kasar
-
Sojojin Sun Gano Wata Mota A Cikin Kududdufin Hakar Ma'adinai A Jihar Plato
Oct 03, 2018 11:50Tawagar sojoji wadanda aka dorawa nauyin gano Manjo-Janar Idris Alkali mai ritaya sun fito da wata mota a cikin kududdufin hakar ma'adinai a garin Dura-Du a karamar kuhumar Jos ta Kudu a jihar ta Plato
-
Gwamnatin Tarayyar Najeriya Ta Rage Kudin Rijistan Kananan kamfanoni Da Kashi 50%
Oct 03, 2018 11:49Gwamnatin tarayyar Najeriya ta rage kudin rigistar kananan kamfanoni da kashi 50% cikin
-
Shugaban Najeriya Ya Ce Kasar Tana Kan Turban Da Ta Dace A Lokacin Shugabancinsa
Oct 01, 2018 19:02Shugaban tarayyar Najeriya Mohammadu a jawabinsa na bikin cika shekaru 58 da samun 'yencin kan kasar ya bayyana cewa gwamnatinsa ta sanya kan kan hanyar da ta dace.