Najeriya : Yan Takara 12 Ke Zawarcin Shugabancin PDP
A yau Asabar ce 6 ga watan Octoba ake saran jam'iyyar PDP, jam'iyyar adawa mafi girma a tarayyar Najeriya za ta fidda dan takara guda daga cikin mutane 12 da suke neman tikitin takarar shugabancin kasa karkashin tutar jam'iyyar a shekara mai zuwa.
Jaridar Punch ta najeriya ta bayyana cewa tun daren jiya jumma'a ce masu neman tikitin na PDP suka fara isa birnin Port Harcourt, na Jihar Rivers in ake saran wakilai 4000 na jam'iyyar zasu zabi wanda zai tsayawa jam'iyyar takarar shugaban kasa a zaben shekara mai zuwa. Wasu yan jam'iyyar suna ganin kafin a fara zaben wasu yan takara daga mutane 12 zasu janyewa wasu.
Amma a takardan da aka mikawa shuwagaban jam'iyyar ta kasa Sanata Ahmad Makarfi, ye zuwa jiya da dare sun hada da tsohon shugaban kasa Atiku Abubakar, gwamnan Sokoto Aminu Tambuwal, Gwamnan Gombe Ibrahim Dankwambo, tsohon gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa kwankwaso, Tsohon gwamnan Sokoto Attahiru Bafarawa.
Sauran sun hada da shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki, tsohon shugaban Majalisar Dattawa David Mark, Alhaji Tanimu Turaki tsohon Ministan ayyuka na musaman, Tsohon gwamnatin Plato Sanata Jona nJang, tsohon gwamnan Kaduna Senata Ahmad Makarfi, tsohon gwamnan Jagawa Sule Lamido da Kuma Dr. Datti Baba-Ahmad.
Majiyar 'yansanda ta kasa ta ce ta tura jami'anta dubu 12,800 don tabbatar da cewa an gudanar da taron na yau lami lafiya.