Gwamnatin Tarayyar Najeriya Ta Rage Kudin Rijistan Kananan kamfanoni Da Kashi 50%
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i33455-gwamnatin_tarayyar_najeriya_ta_rage_kudin_rijistan_kananan_kamfanoni_da_kashi_50
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta rage kudin rigistar kananan kamfanoni da kashi 50% cikin
(last modified 2018-10-03T11:49:31+00:00 )
Oct 03, 2018 11:49 UTC
  • Gwamnatin Tarayyar Najeriya Ta Rage Kudin Rijistan Kananan kamfanoni Da Kashi 50%

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta rage kudin rigistar kananan kamfanoni da kashi 50% cikin

Kamfanin dillancin labaran gwamnatin Najeriya NAN ya nakalto jami'a mai kula da lamura na musamman na mataimakin shugaban kasa Prof. Yeme Osinbajo, Laolu Akande yana fadar haka a jiya. Ya kuma kara da cewa Prof. Osinbajo ya bayyana haka ne a taro na 19Th na kananan masana'antu na kasar wanda aka gudanar a birnin Enugu. 

Labarin ya kara da cewa wannan ragin daga Naira dubu gome zuwa dubu 5 zai yi aiki ne na tsawon kwanaki 90 don bawa marasa sa karfi rigistan masana'antunsu, wanda zai basu damar samun tallafin gwamnati a duk lokacinda ta sami damar  yin hakan. 

Ya ce rigin ya fara ne daga ranar daya ga watan Octoba har zuwa karshen watan Decemba mai zuwa.