Najeriya : Buhari Ya Godewa APC
Shugaba Muhammadu Buhari na tarayyar Najeriya a jawabin da ya gabatar a taron jam'iyyarsa ta APC a Abuja a jiya da dare ya godewa yan jam'iyyar da suka amince da shi a matsayin dan takara tilo a zaben fidda gwani na dan takara shugaban kasa a karkashin tutar jam'iyyar na zaben shekara mai zuwa.
Kamfanin dillancin labaran Nan na Najeriya ya nakalto shugaban yana ambatar wasu ayyukan ci gaba da gwamnatinsa ta samu a cikin shekaru kimani 4 da suka gabata wadanda suka hada da kyautatuwan tsaro a kasar, da kuma raguwar cin hanci da rashawa da kuma satar kudaden jam'a.
A birnin Fatakwal na jihar Rivers kuma babban jam'iyyar adawar kasar tana ci gaba da taronta na fidda goni daga cikin yan takara da suke neman tikitin shiga takarar shugaban kasa a zaben na shekara mai zuwa.
Sakamakon zaben da wasu kakafen yana labarai sun bayyana ya nuna cewa Bokola Saraki kakakin majalisar dattawan kasar shi ne a gaba da kuri'u 317. ana saran za'a bayyana cikken sakamakon zaben a yau Lahadi. Wakilai daga jihohi 36 na kasar 3,274 ne suka kada kuri'unsu a zaben fidda gonin.